Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA- Mataimakin farko na shugaban majalisar, Omar Boshah, ya fada a wani taron manema labarai a birnin Tripli cewa akwai yiwuwar duk shirin da ake ya rushe, idan aka tafi zaben a lokacin da aka tsara saboda rikici da kuma rashin yarda tsakanin bangarorin da kuma shishigi na kasashen ketare.
Ya kara da cewa idan aka gudanar da zabe a ranar 24 ga watan Disamba, to kuwa tabbas ba za’a amince da sakamakon zaben, don haka ne majalisar ta bukaci a gudanar da zaben shugaban kasar tare da na ‘yan majalisa a watan Fabarairu.
Yau dai kusan mako biyu a je zaben, amma har yanzu ba’a fitar da jerin sunayen ‘yan takaran da zasu fafata a zaben ba.
342/